<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>John Henry Yates, Ira David Sankey</author>
<hymn_number>286</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Shi Yesu ne Mai Nasara a bisa Maƙiyi.
 Tun ran da aka giciye shi, ya ka da zunubi.
 Ya gama aiki duk a can, ya kawo gafara, Sai mu mu ba da gaskiya ga Ubangijinmu.

[V2]
 KORUS
 Ta wurin bangaskiya na sami nasara,
 Ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.

[V3]
 2) Yanzu mu Masu Bill Yesu mun sami gafara.
 Kada mu rasa nasara a bisa Makiyi.
 Ba za mu bauta wa Shaidan, mu saurare shi ba.
 Zunubi ba zai ka da mu, ya kai mu mutuwa ba.
 Korus

[V4]
 3) Yesu shi ne mai mulkinmu a cikin duniya,
 Mu sa kanmu a hannunsa, mu nemi nufinsa.
 Abin da ya ke so mu yi, mu yi da zuciya daya
 Don kada zvnubi ya zo, ya rinjaye mu dai.
 Korus</lyrics>
<title>Shi Yesu Ne Mai Nasara A Bisa Maƙiyi LW286</title>
</song>